Home Labaru Gwamna Zulum Ya Raba Tallafin Kayan Abinci Ga Magidanta 13,000 A Gwoza

Gwamna Zulum Ya Raba Tallafin Kayan Abinci Ga Magidanta 13,000 A Gwoza

281
0

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya jagoranci
raba kayan tallafin kayan abinci ga magidanta dubu 13,
wadanda matsalar harin Boko Haram ta shafa a garin Gwoza.

Raba kayan tallafin abincin dai ya gudana ne, a fargajiyar kofar Fadar Sarkin Gwoza Mai Martaba Shehu Idrissa Timta.

Gwamna Zulum, ya shiga garin Gwoza ne ranar Asabar da ta gabat, inda ya kai wata ziyarar ba-zata a babban asibitin garin da tsakar dare, inda biyo bayan samun asibitin cikin duhu ya bada umurnin daukar matakin gyara nan take.

A Ranar Lahadin da ta gabata, Zulum ya jagoranci kaddamar da raba kayan tallafin ga mabukata, inda kowane mutum daya daga cikin adadin magidanta dubu 13 ya samu tallafin buhun shinkafa da na masara.

Leave a Reply