Home Labaru Shugabancin APC: Kyari Ya Maye Gurbin Adamu

Shugabancin APC: Kyari Ya Maye Gurbin Adamu

34
0

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa Abubakar
Kyari, ya maye gurbin Sanata Abdullahi Adamu a matsayin
sabon shugaban jam’iyyar na ƙasa.

Wannan sauyi da jam’iyyar APC ta samu dai ya yi daidai da tanadin kundin dokokin ta, wanda ya nuna cewa idan shugaban jam’iyyar na ƙasa ya yi murabus mataimakin sa ya maye gurbin sa a matsayin na riƙon ƙwarya.

Rahotanni sun ce tuni Abubakar Kyari ya jagoranci taron ‘yan Kwamitin Gudanarwa na jam’iyyar a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja.

Daga cikin mahalarta taron dai akwai Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa a yankin Kudu Emma Enukwu, da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa a yankin Arewa maso Yamma Salihu Lukman da na yankin Arewa maso Gabas Salihu Mustapha.

Abdullahi Adamu dai ya miƙa wa Fadar Shugaban Ƙasa wasiƙar ajiye muƙamin sa, yayin da ya rage ‘yan sa’o’i kafin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da zai gudana a ranakun Talata da kuma Laraba.

Leave a Reply