
Babban Daraktan gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Aminu Waziri Tambuwal, ya ce jam’iyyar sa ta fi jam’iyyar APC sau dubu.
Tambuwal, ya bayyana dalilin da yasa PDP ce jam’iyyar da tafi dacewa da zama zabin ‘yan Nijeriya a zaben shekara ta 2023, inda ya ce yayin da PDP ta nuna adalci a tikitin ta na takarar shugaban kasa, tikitin jam’iyyar APC bai nuna dabi’ar tarayya ta Nijeriya ba.
Ya ce jam’iyyar APC ta haifar da sabani a Nijeriya, ya na mai cewa PDP za ta yi aiki domin tabbatar da ganin irin haka bai sake faruwa ba.
Gwamnan Tambuwal ya bayyana haka ne, a wajen kaddamar da gangamin yakin neman zaben jam’iyyar PDP a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom.













































