Home Labaru Gwamna Lawal Ya Nemi Haɗin Kan NADDC Don Horar Da Matasan Zamfara

Gwamna Lawal Ya Nemi Haɗin Kan NADDC Don Horar Da Matasan Zamfara

1
0

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, ya nemi haɗin kan
cibiya ƙirƙire-ƙirƙire d tsara motoci ta ƙasa da ke Abuja,
domin horar matasan Jihar da zummar kyautata rayuwar su.

Dauda Lawal ya buƙaci haka ne yayin da ya kai ziyara a cibiyar, inda ya samu tarba daga Shugaban cibiyar Jelani Aliyu tare da wasu manyan jami’an sa.

Gwamna Dauda, ya ce a shirye Jihar Zamfara ta ke domin haɗa kai da cibiyar wajen ba matasan jihar ilimin da za su iya dogaro da kan su.

Da ya ke jawabi yayin ziyarar, Dauda Lawal ya ce sun je ne domin neman damar da za su ƙara wa jihar Zamfara ƙaimi, domin wamnati ta gano fannoni masu muhimmanci da su ka haɗa da tsaro da harkar ilimi da harkar noma da koyar da sana’o’i da kuma bunƙasa matasa.

Ya ce ya fahimci cewa cibiyar ta buɗe sashen bada horo a Gusau wadda ba a riga da an ƙaddamar da ita ba, don haka gwamnatin shi za ta bada duk gudunmawar da ake buƙata domin tabbatar da ganin an ƙaddamar da ita kuma ta fara aiki.