Home Labaru Gwamna Dikko Ya Amince Da Bude Asusun Bai-Daya A Jihar Katsina

Gwamna Dikko Ya Amince Da Bude Asusun Bai-Daya A Jihar Katsina

79
0

Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda, ya
amince da fara amfani da asusun bai-daya domin tabbatar da
gaskiya da adalci a ayyukan gwamnati.

A kan wannan ne, gwamnatin jihar ta dakatar da dukkan hada- hadar kudade ta asusun ajiya na kudaden shiga daga ma’aikatu da sassa da hukumomi daban-daban.

Mataimakin gwamnan jihar Katsina Malam Faruk Lawal Jobe ya bayyana haka, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a cibiyar ‘yan jarida da ke Katisna.

Lawal Jobe, ya ce an shirya taron manema labarai ne domin yin karin haske a kan manufofi da tsare-tsaren gwamnati, inda ya ce ya zama wajibi duk kudaden shigar da jihar ta samu a zuba su zuwa asusun bai-daya, yayin da ma’aikatu da sassa da hukumomi ya zama dole su nemi izini kafin su cire kudi.

Ya ce za a kafa kwalejin ma’aikata domin horar da ma’aikatan gwamnati, kuma ya zama wajibi ga ma’aikaci daga mataki na 13 ya rubuta jarrabawa kafin a yi masa karin girma zuwa mataki na gaba.

Leave a Reply