Home Labaru Kiwon Lafiya Kwararar Hamada: Gwanatin Tarayya Ta Dasa Itatuwa Sama Da Miliyan 10 A...

Kwararar Hamada: Gwanatin Tarayya Ta Dasa Itatuwa Sama Da Miliyan 10 A Jihohi 11

109
0

A ci-gaba da ƙoƙarin magance matsalar kwararowar hamada a
wasu jihohin ƙasar nan, Gwamnatin Tarayya ta hannun
Hukumar Kula da Matsalar Hamada ta Ƙasa ta dasa itatuwa
sama da miliyan 10 a jihohi 11 na Nijeriya.

Shugaban Hukumar Kula da Kwararar Hamada Dakta Yusuf Maina Bukar ya bayyana haka, a wajen bikin zagayowar ranar dashen itatuwa a Gusau, babban birnin jihar ranar Alhamis.

Dakta Bukar, wanda ya samu wakilcin Daraktan Gudanarwa na hukumar Nasiru Ismail, ya ce jahohi 11 da kwararar hamada ta shafa sun hada da Sokoto da Kebbi da Katsina da Zamfara da Kano da Jigawa da Bauchi da Gombe da Yobe da Borno da kuma Adamawa.

Ya ce hukumar ita ce cibiyar da Nijeriya ta maida hankali wajen ganin an cimma manufar Ƙungiyar Tarayyar Afirka domin sauya yanayin sahara da kuma yankin sahel.

Ya kuma yi nuni da cewa, hukumar ta sanya ranar 13 ga watan Yuni na kowace shekara domin gudanar da bikin yaƙi da kwararar hamada a Nijeriya.

Leave a Reply