Home Ilimi Gwamanati Ba Za Ta Biya Malaman Jami’a Albashinsu Na Wata Shida Ba

Gwamanati Ba Za Ta Biya Malaman Jami’a Albashinsu Na Wata Shida Ba

191
0

  

Ministan ilimi Malam Adamu Adamu ya ce batun biyan malaman jami’o’i albashinsu na tsawon watannin da ba su yi aiki ba shi ne kaɗai abin da ya rage ba a cimma ba a yarjejeniyar ASUU da gwamnati.

Minsitan ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Sannan Malam Adamu Adamu, ya ce hakkin malaman jami’o’i ne su biya ɗalibai diyya saboda ɓata musu lokacin da suka yi tsawon wata shida a yayin da suke yajin aikin da ba gwamnati ta sa a yi shi ba.

Adamu Adamu, ya ce ya kamata daliban da yajin aikin ya shafa su kai kungiyar kotu don neman fansa a kanzaman banzan da aka tilasta musu a gida.

Leave a Reply