Home Labaru Gwabza Yaki: Sojojin Afghanistan Sun Fatattaki Mayaƙan Taliban Daga Lashkar Gah

Gwabza Yaki: Sojojin Afghanistan Sun Fatattaki Mayaƙan Taliban Daga Lashkar Gah

51
0

Jami’an sojan Afghanistan sun ce sun yi nasarar fatattakar
mayaƙan Taliban daga kudancin birnin Lashkar Gah da ke lardin
Helmand.

Wani kwamandan yankin ya ce sun yi wa mayaƙan mummunar
ɓarna.

Rahotanni sun nuna cewa mayaƙan sun kutsa kusa da tsakiyar
birnin ne ranar Juma’a.

Lashkar Gah, shi ne babban birnin lardin na biyu da ‘yan Taliban
suka samu shiga a cikin ‘yan kwanakin nan.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce fararen hula fiye da 200 sun ji
rauni a faɗan da aka yi a cikin mako biyu da suka gabata a kusa
da birnin Kandahar.