Home Labaru Guraben Aiki: Ma’aikatan ‘N-Power’ 500 Sun Ajiye Aiki A Jihar Zamfara

Guraben Aiki: Ma’aikatan ‘N-Power’ 500 Sun Ajiye Aiki A Jihar Zamfara

589
0

Akalla ma’aikatan shirin tallafi na N-Power 500 ne su ka ajiye aiki a Jihar Zamfara bayan sun samun aiki na dindindin, kamar yadda jami’in shirin na Jihar Zamfara Kabiru Umar ya bayyana.

Umar ya bayyana haka ne, a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai a Gusau, inda ya ce wadanda su ka ajiye ayyukan su sun samu aiki ne a karkashin gwamnatin tarayya da ta jiha da wasu hukumomi daban-daban.

Ya ce an dauki ma’aikatan N-Power har dubu 11 da 122 tsakanin shekara ta 2016 zuwa 2017 a jihar Zamfara.

Umar ya kara da cewa, wasu ma’aikatan sa-kai 321 ma an dauke su a karkashin shirin N-Power, inda su ka yi ayyukan na’urorin kwamfuta da sauran fasahohin da su ka danganci zamani.

Sai dai ya yi tsokacin cewa, saboda rashin wadatattun motoci akwai matsala sosai wajen yadda za a iya bi gari-gari ana yin duba-garin ayyukan ma’aikatan a karkashin shirin na N-Power.