Home Labarai Dakatar Da Sanata Ningi: Jam’Iyyun Hamayyar Najeriya Sun Mayar Da Martani

Dakatar Da Sanata Ningi: Jam’Iyyun Hamayyar Najeriya Sun Mayar Da Martani

75
0

Jam’iyyun hamayya a Najeriya sun yi Allah-wadarai da matakin da majalisar dattawa ta dauka na dakatar da Sanata Abdul Ningi na tsawon wata uku, bayan da ya yi wasu kalamai da ke nuna an cusa wasu kudi naira kusan tiriliyan hudu, wadanda ba a san inda aka nufa da su ba a kasafin kudin bana.

Jam’iyyun hamayyar suna ganin kamata ya yi a fara da gudanar da bincike kan batun cushen kudin, domin a tabbatar da gaskiya ko akasin zargin, kafin a dauki matakin dakatar da dan majalisar.

Jam’iyyar sa ta PDP, ta bayyana matakin a matsayin wani yunkuri na hana gudanar da bincike, da yin rufa-rufa, da kuma kawar da hankalin ‘yan Najeriya kan batun da sanatan ya bankado.

Jam’iyyar ta ce tana goyon bayan Sanatan nata game da matakin da ya dauka na yayata badakalar da yake zargin an yi, a cewar Ibrahim AbdulLahi, mukaddashin jami’in hulda da jama’a na kasa na jam’iyyar PDP.

Matakin dakatar da Sanata Abdul Ningi, na tsawon wata uku da majalisar dattawan ta dauka, na ci gaba da shan suka, har ma bakin wasu jam’iyyun hamayya ya zo daya, wajen yin tir da lamarin.

Leave a Reply