Home Labaru Gbajabiamila Ya Sauka Daga Kujerar Ɗan Majalisa

Gbajabiamila Ya Sauka Daga Kujerar Ɗan Majalisa

402
0

Tsohon shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ya
sauka daga kujerar sa domin fara aiki a sabon muƙamin sa na
shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa.

Sabon shugaban majalisar Tajudeen Abbas ne ya karanto wasiƙar ajiye aiki a zauren majalisar.

Femi Gbajabiamila dai ya samu nasara a zaɓen kujerar ɗan majalisar wakilai, inda aka yi ta nuna damuwa kan yadda zai tafiyar da muƙaman biyu, bayan ya ƙarbi rantsuwa tare da sauran ‘yan majalisar har ma ya jefa ƙuri’ar sa a zaɓen shugabannin majalisar.

Yanzu dai hukumar zaɓe mai zaman kan ta ta kasa za ta shirya zaɓen cike-giɓi na ɗan majalisar wakila mazaɓar Gbajabiamila.

LEAVE A REPLY