Home Labaru Gbajabiamila Da Wase Sun Tofa Wa Juna Miyau A Zauren Majalisa

Gbajabiamila Da Wase Sun Tofa Wa Juna Miyau A Zauren Majalisa

95
0

An samu saɓani tsakanin Kakakin Majalisar wakilai Femi
Gbajabiamila da mataimakin sa Idris Wase, inda ta kai su ga
yin fito-na-fito da juna.

Tsawon shekaru huɗu huɗu dai ba a taɓa samun saɓani tsakanin shugabannin biyu ba, sai a yanzu da Idris Wase ya fito ƙarara ya na neman takarar Kakakin Majalisar.

Lamari dai ya dagule ne yayin rufe zaman Majalisa na ranar Larabar da ta gabata, yayin da Gbajabiamila ya umarci Shugaban Kwamitin Bin Ƙa’idoji na majalisa Hassan Fulata ya rubuta lokacin tashi daga Majalisa, saboda ya na son halartara wani taro, inda nan take Idris Wase ya ce lamarin Gbajabiamila ya zama abin dariya.

Ya ce bai kamata a ture muhimman batutuwan da ke gaban majalisa ba saboda kawai Gbajabiamila ya na so ya halarci wanilamari na daban ba, don haka duk mai son taɗiya wurin wani taro ya tashi ya tafi, amma babban abin da ke gaban su shine aikin da su ke yi wa ‘yan Nijeriya waɗanda.

Gbajabiamila, ya ce tun da ake dimokraɗiyya a Nijeriya babu mataikakin da ya taɓa yin fito-na-fito da Kakakin Majalisa sai Idris Wase.

Leave a Reply