Home Labaru Kiwon Lafiya Ma’Aikatan Lafiya Sun Tsunduma Yajin Aiki

Ma’Aikatan Lafiya Sun Tsunduma Yajin Aiki

1
0

Ma’aikatan lafiya a karkashin kungiyar hadin gwiwa ta fannin
kiwon lafiya JOHESU sun fara yajin aikin sai baba-ta-gani.

Mataimakin shugaban kungiyar na kasa Ogbona Chimela ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a Abuja.

Ogbona Chimela, ya ce sakamakon nuna son zuciya da nuna halin ko in kula da ma’aikatar lafiya ta tarayya ne ya sa su ka shiga yajin aikin.

Ya ce batun da ake takaddama a kai shi ne, gyara tsarin albashi na ma’aikatan lafiya da biyan wasu alawus-alawus ga ma’aikatan, don haka ma’aikatan kiwon lafiyar sun bukaci a aiwatar tare da daidaita al’amurra idan har ana bukatar su koma bakin aiki.

Ma’aikatan, sun kuma bukaci amincewar ma’aikatan lafiya a cibiyoyin da ba na asibiti ba wajen biyan sabon alawus- alawus.