Home Labarai Zawarcin ‘Yan Wasa: PSG Na Son Rashford Da Diaz Don Maye Gurbin...

Zawarcin ‘Yan Wasa: PSG Na Son Rashford Da Diaz Don Maye Gurbin Mbappe, Arsenal Na Neman Gola

114
0

Paris St-Germain na shirin taya Marcus Rashford fam miliyan 80, kuma kungiyar ta ce a shirye take ta rika biyan dan gaban na Manchester United da Ingila albashin kusan fam dubu 500 a mako.

Haka kuma PSGn na son dan wasan gaba na gefe na Liverpool kuma dan Colombia Luis Diaz, mai shekara 27 domin maye gurbin Kylian Mbappe, wanda ake sa ran zai tafi Real Madrid.

A shirye shugaban Chelsea Todd Boehly yake ya sayar da Romelu Lukaku, wanda ke zaman aro a Roma, da kuma mai tsaron ragar Sifaniya Kepa Arrizabalaga, wanda shi kuma yake zaman aro a Real Madrid, ga kungiyoyin gasar Saudiyya a bazara domin samun fam miliyan 100 daga cinikin ‘yan wasa.

Masu nema wa Manchester United ‘yan wasa sun fara rangadin manyan kungiyoyin Turai, kafin bude kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa, domin ta san ‘yan wasan da za ta saya tun da wuri a bazaran nan.

Leave a Reply