Iyalan Mataimakin shugaban kungiyar Fulani ta Meyyati a Najeriya Munir Atiku na kira ga gwamnati da Hukumomin tsaro da daidaikun mutane su taimaka a bayyana masu inda yake.
Iyalan Sun bayanna hakan ne a cikin wata sanarwa da suka rabawa manema labarai, inda suka bukaci ganin Hukumomin da abinda ya shafa Sun dauki mataki na ganin sun gano inda yake.
Daya daga cikin Yayansa Mai Suna Abdullahi Balarabe, ya ce rabon da su sashi mahaifinsu a Ido tun a watan Yuni na shekara ya 2023, Lamarin da ya tayar mash da hankali.
Ya ce bar gida a Katsina domin zuwa kaduna inda suka Tabbatar da cewar an yi Gmgarkuwa da shi ne a tsakanin hanyar Zaria zuwa Kaduna.
Abdullahi Balarabe ya ce a halin yanzun iyalnasa na cikin gagari saboda Rashin ganinta da Kuma samun bayanai na halinda yake cikin, lamarinda suka ce ya sa su cikin.mummunan Yanayi.
Ya tabbatar da cewar Rashin ganinsa da Kuma samun labarin.inda yake yaje su cikin dimuawa da damuwa tare da snyawasu cikin duhu akan makomarasa.
Daga Karshe ya ce Suna bukatar hukumomjn tsaro su yi dukkanin Mai yiyuwa wajen ganin an Gano halinda yake Ciki tare da kubutR da shi.