Shugaban Hukumar Zaɓe mai zaman kan ta ta Ƙasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya gargaɗi sabbin Kwamishinonin Zaɓe su nisanci shiga harkokin siyasa ko yin tarayya da ‘yan siyasa ba bisa ƙa’idar da doka ta tanada ba.
Farfesa Yakubu, ya ce Kwamishinonin su tabbatar su na bin dukkan tsare-tsaren da dokar zaɓe ko dokar ƙasa ta shimfiɗa wajen gudanar da aikin su.
Mahmud Yakubu ya yi gargaɗin ne, a lokacin da ya ke rantsar da sabbin Kwamishinonin Zaɓen 19, inda ya ce ya zama dole su kasance su na aiwatar da komai a kan ƙa’ida ba tare da nuƙu-nuƙu ko fifita wani ɓangare ba, kuma a duk lokacin da su ke ganawa da masu ruwa da tsaki su kasance ba su wuce ƙa’idar da dokar ƙasa ta gindaya masu ba.
Farfesa Mahmud Yakubu, ya gargadi sabbin Kwamishinonin su nisanci kai ziyara ofishin gwamna, domin ba a so a gan su gidan gwamnati, kuma kada su riƙa keɓewa su na ganawa da ‘yan siyasa ba bisa ƙa’idar aikin ofis ba.
A karshe ya jaddada masu cewa, hanyar amfani da tsarin tantance sahihiyar rajistar zaɓe ta BVAS ce kaɗai hanyar da aka amince a tantance mai rajistar zaɓe.
You must log in to post a comment.