Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai halarci taron a kan sauyin yanayi da zai gudana a garin Sharm El-Sheikh na ƙasar Masar ba.
Buhari ya umarci Ministan Muhalli Mohammed Abdullahi ya wakilce shi a wajen taron, wanda zai gudana daga ranar 6 zuwa 18 ga watan Disamba na shekara ta 2022.
Ministan zai jagoranci tawagar Nijeriya a ɓangarorin taron sannan ya karanta jawabi, zai kuma halarci tarurruka game da shirin Nijeriya na sauya alƙiblar makamashin ta.
Sauran ministoci biyar da za su yi wa ministan rakiya sun hada da Ministar Kuɗi Zainab Ahmed, da Ministan Lantarki Abubakar Aliyu, da Ministar Agaji Sadiya Farouq, da Ministan Noma Mohammad Mahumud Abubakar da kuam Ministan Ruwa Suleiman Hussein Adamu.














































