Home Labaru Ganduje Ya Koka A Kan Zaman Tinubu Da Kwankwaso A Faransa

Ganduje Ya Koka A Kan Zaman Tinubu Da Kwankwaso A Faransa

305
0

A wani faifan murya da ake zargin gwamna Abdullahi Umar
Ganduje na jihar kano ne ya ke bayani, an ji gwamnan ya na
korafi dangane da ganawar Bola Tinubu da Kwankwso a
kasar faransa.

Rahotanni sun ce ta ce Ganduje bai ji dadin yadda Bola Tinubu ya kebe da abokin gabar sa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ba a kasar waje ba.

A faifen muryar mai tsawon mintina hudu da ke yawo, ana Gwamna Ganduje ya kai kukan sa ne wajen Ibrahim Kabir Masari.

Gwamna Ganduje dai ya nuna ba a yi ma shi adalci ba, yayin da Ibrahim Masari ya ke ba shi hakuri ya nuna ma shi ya je su zauna don bai dace a rika maganar a waya ba.

Ganduje ya fara da shaida wa Masari cewa ana ta surutu ko ina a cikin Kano saboda zaman da Tinubu ya yi da Kwankwaso a birnin Paris.

Leave a Reply