Tsohon Gwamnan Jihar Kano Abdulahi Umar Ganduje, ya
bukaci Babbar Kotun Jihar ta hana Hukumar Yaki da cin
hanci da Rashawa EFCC ci-gaba da binciken sa a kan bidiyon
Dala.
A shekara ta 2018 ne, jaridar Daily Nigerian ta wallafa wasu faya-fayan bidiyo, inda a ciki ake zargin Ganduje da karbar cin hanci da Dalar Amurka daga hannun wasu ‘yan kwangila.
Sai dai a kwafin wata kara da Ganduje ya shigar, ya nemi kotun ta bayyana cewa bisa tanadin Kundin Tsarin Mulki, haramun ne EFCC ta binciki lamarin da tuni ya ke gaban Majalisar Dokoki ta Jihar.
An dai shigar da karar ne a ranar 23 ga watan Maris, kwanaki kadan kafin tsohon Gwamnan ya mika ragamar mulki ga sabuwar gwamnati, sannan bincike ya nuna cewa an kai wa hukumar EFCC takardun kotun ne a ranar 5 ga watan Maris.