Home Labarai Fulani Da Irigwe Sun Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Fulani Da Irigwe Sun Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya

374
0

Al’ummomin Fulani da Irigwe da ke Karamar Hukumar Bassa ta Jihar Filato, sun sanya hannu a kan jarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin su.

Shugabannin kabilun biyu sun sanya hannu a kan yarjejeniyar ne a gaban Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong a gidan gwamnatin jihar da ke garin Jos.

Yankin Bassa dai ya kwashe shekara da shekaru ya na fama da rikice-rikice tsakanin al’ummomin Fulani da kablar Irigwe.

Da ya ke jawabi yayin taron sanya hannu a kan yarjejeniyar, Gwamnan Lalong ya bayyana farin cikin sa da matakin da al’ummomin su ka dauka, inda ya ce sun nuna wa duniya cewa sun gaji da rikice-rikice a yankin su, don haka su ka kudiri aniyar yafe wa juna domin kare faruwar rikici-rikice a nan gaba.

Sarkin Miango Rebaran Ronku Aka, ya gode wa Gwamna Lalong a kan kokarin sa na ganin an samu zaman lafiya a yanki da ma jihar Filato baki daya.

Leave a Reply