Home Labarai Fubara Ya Ce Sun Gaji Bashin Sama Da Naira Biliyan 200 A...

Fubara Ya Ce Sun Gaji Bashin Sama Da Naira Biliyan 200 A Jihar

92
0
Gov. Siminalayi Fubara of Rivers
Gov. Siminalayi Fubara of Rivers

Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa gwamnatin sa ta gaji wasu ayyuka da ba a kammala a ƙananan hukumomi 13 na jihar.

hakan na zuwa ne a lokacin da yake ƙaddamar da wani asusun gudanar da aiki domin bikin cika shekara guda da hawa kan mulki,

ya bayyana cewa, a karkashin jagorancin sa, gwamnatin jihar Ribas ta bayar da wasu sabbin ayyukan tituna wadanda kudin su ya kai naira biliyan 534.332.

Ya bayyana rikicin siyasar da ya ɓarke tsakanin sa da ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesome Wike,

cikin wata uku da hawar sa kan karagar mulki a matsayin wani mummunan alamari.

gwamnan ya tabbatar da cewa yanayi mafi muni ya wuce, domin gwamnatin sa ta samu nasarar kare hakkin ta na gudanar da mulkin jihar tare da tabbatar da ci gaban ta cikin ‘yanci,

Gwamna Fubara ya yi nuni da cewa, tun bayan rikicin, abubuwa da dama sun canja a fagen siyasa,

kuma ya ci gaba da tsayawa tsayin daka kan alkawarin da ya ɗauka shekara guda da ta wuce na ba jihar Ribas fifiko,

da kare muradun ta, da tabbatar da cewa al’ummar jihar sun samu ramon dimokuradiyya da shugabanci na gari.

Leave a Reply