Majalisar Dattawa ta gabatar da kudurin dokar kare daliban jami’o’i mata daga cin zarafin, biyo bayan rahoton binciken da kafar yada labarai ta BBC ta yi, inda ta bankado yadda wasu malaman jami’a ke fasikanci da dalibai mata a kasashen Nijeriya da Ghana.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ovie Omo-Agege da ya gabatar ta kudurin, ya ce rahoton BBC zai taimaka wa kudirin dokar samun goyon baya.
Idan dai ‘yan majalisar su ka amince kudurin ya zama doka, zai haramta wa malaman jami’a yin kowane nau’in neman yin fasikanci da daliban su.
A
karkashin dokar, an tanadi daurin da ya kai na tsawon shekaru 14 ga duk malamin
da aka kama da laifin yin mu’amalar jinsi da wata daliba.
You must log in to post a comment.