Home Home Fasa Kwauri: Hukumar NAFDAC Ta Kama Ganda Ta Miliyan 23 A Legas

Fasa Kwauri: Hukumar NAFDAC Ta Kama Ganda Ta Miliyan 23 A Legas

110
0
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya wato NAFDAC ta kama tan 120 na ganda mai ɗauke da sinadarai wadda aka shigo da ita Najeriya.

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya wato NAFDAC ta kama tan 120 na ganda mai ɗauke da sinadarai wadda aka shigo da ita Najeriya.

A wani labari da hukumar ta fitar a shafinta na Twittera  ranar Lahadi, ta bayyana cewa an kama gandar ce a wurare shida a Legas.

Shugabar hukumar ta NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ta bayyana cewa mutum bakwai da ake zargi da wannan lamarin ana gudanar da bincike a kan su.

Ta bayyana cewa tuni aka ɗauki samfarin gandar domin kai ta ɗakin gwaji domin gano ingancin ta.

Ta ce an yi ƙiyasin farashin gandar kan kusan naira miliyan 23.