Home Labaru Kasuwanci Farashin Litar Man Fetur Ya Kai ₦560 A Kasar Ghana

Farashin Litar Man Fetur Ya Kai ₦560 A Kasar Ghana

173
0

Ana ci gaba da samun hauhawar farashin man fetur a kasar Ghana, inda farashin ya yi tashin gwauron zabi zuwa kusan sidi 7 kwatankwacin Naira 560 na Najeriya.

Wannan Lamarin dai ya sa direbobin motocin haya bai wa gwamnatin kasar wa’adin nan da ranar Litinin mai zuwa domin janye haraji a kan man fetur da dangoginsa, ko kuma su tsunduma yajin aiki.

Gwamnatin kasar ta saka Haraji nau’i takwas a kan man fetur, amma waɗanda suke ci wa direbobin tuwo a kwarya, guda uku ne.

Direbobin sun kuma bukaci gwamnati ta janye su da nufin kawo sauƙi ga rayuwar al’ummar kasar ta Ghana.