Home Labaru Farar Fata Na Karshe Da Ya Shugabanci Afirka Ta Kudu Ya Mutu

Farar Fata Na Karshe Da Ya Shugabanci Afirka Ta Kudu Ya Mutu

205
0

FW de Klerk, tsohon shugaban Afirka Ta Kudu kuma farar fata na karshe da ya jagoranci kasar, ya mutu yana da shekaru 85.

Mr de klerk, wanda jigo ne a yunkurin kasar na komawa turbar dimokuradiyya, an gano ya kamu da cutar daji a wannan shekarar.

FW de Klerk ya shugabanci kasar daga watan Satumbar 1989 zuwa watan Mayun 1994.

A shekarar 1990 ne ya bayyana cewa zai saki shugaban masu rajin yaki da mulkin wariyar launin fata Nelson Mandela, lamarin da ya kai ga yin zabe mai jam’iyyu da dama a shekarar 1994.

Wata sanarwa da Gidauniyar tsohon shugaban kasar FW de Klerk ta fitar aAlhamis din nan da safe ta ce tsohon shugaba FW de Klerk ya mutu cikin lumana a gidan sa da ke Fresnaye Cape Town da sanyin safiya bayan ya yi fama da cutar daji ta huhu.

Ya bar matar sa e Elita, da ‘ya’yan sa Jan da Susan da kuma jikokin sa.

Leave a Reply