Home Labaru Kasuwanci Tashin Farashin Shinkafa: Ministar Kudi Ta Ce Masu Fasa Kwauri Ne Ummmul’aba’isi

Tashin Farashin Shinkafa: Ministar Kudi Ta Ce Masu Fasa Kwauri Ne Ummmul’aba’isi

146
0

Ministar Kuɗi Zainab Ahmed ta ce masu fasa ƙwauri ne ke jawo tashin farashin shinkafa a kasuwannin ƙasar.

Da take magana a shirin Talabijin na Channels a ranar Alhamis, ministar ta ce ‘yan sumogal ne ke cutar da ‘yan Najeriya ta hanyar shigo da kayan da ba su da inganci.

Ta ce akwai ‘yan ƙasa marasa kishi da ke shigo da shinkafa marasa inganci, wanda bai kamata ɗan Adam ya ci ba, amma haka za su shigo da ita kasuwa su sayar.

Ministar ta jaddada cewa akwai rundunonin haɗin gwiwa da gwamnati ta samar don yaƙi da fasa ƙwauri da kuma daƙile ayyukan masu kawo wa tattalin arzikin ƙasa cikas.

Zainab Ahmad ta ce Gwamnatin Najeriya ta haramta shigar da shinkafa daga ƙasashen waje ne da zimmar haɓaka noman ta a Najeriya.

Leave a Reply