Home Labarai Kwanton Bauna: ‘Yan Ta’Adda Sun Kashe ‘Yansanda 4 A Katsina

Kwanton Bauna: ‘Yan Ta’Adda Sun Kashe ‘Yansanda 4 A Katsina

30
0
NIGERIAN POLICE WITH RIFLE TheCable0 e1638223533511 1280x720 copy
NIGERIAN POLICE WITH RIFLE TheCable0 e1638223533511 1280x720 copy

Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina, ta bayyana cewar wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kashe jami’an ta hud.

Mazauna garin Zandam na karamar hukumar Jibia sun shaida cewa maharan sun far wa dakarun ne a ranar Lahadi.

Kakakin ‘yansandan jihar, ya bayyana cewar ‘yansanda hudu ne suka rasa rayukan su kuma tuni ta tura karin dakaru zuwa wurin.

Irin wannan harin ba shi ne na farko ba a Jihar Katsina, inda ‘yan bindiga ke kashe jami’an tsaro,

sai dai a baya-bayan nan rundunar sojin Nijeriya na samun nasarar kawar da jiga-jigan ‘yan bindiga a Arewa Maso Yammacin Nijeiriya.

Leave a Reply