An shiga halin fargaba a unguwar Nike da ke jihar Enugu a kudancin Najeriya, bayan gwamnati ta fara rusa gidajen mutanedon gina wani sabon birni.
Mai gonar UD da ke unguwar ta Nike, Ngozi DeDe cikin hawaye ta bayyana cewa an kashe mata dabbobin da take kiwo da suka haɗa da kifi da kaji da darajarsu ta kai naira miliyan 30.
Mazauna unguwar da dama sun koka cewa gwamnati ba ta basu wata sanarwa ba kan rushe gidajen nasu, sai kawai ta fara rusau.
Ngozi ta ce a ranar talata sai jami’an hukumomin ma’aikatarEnugu suka fado mana, suka rusa gidan kajin ta , kuma batawata sanarwar ba.
A cewarta a bara gwamnatin ta bayar da takarda, amma ita an gaya mata cewa bata cikin waɗanda abin zai shafa, sai gashi an
zo an rushe mini gidan kaji.
Ngozi Dede, ta ce an kashe mata kaji 30,000 da kifi tarwaɗa 1,000 a gidan kaji uku da tare da lalata mata gidan ma’aikata biyu. Gwamnatin jihar ta Enugu ta sanya hannu a wata takarda na gina wani sabon birni a unguwar ta Nike.














































