Home Home Kwastam Za Ta Raraba Wa ‘Yan Nijeriya Shinkafa Da Sauran Kayan Da...

Kwastam Za Ta Raraba Wa ‘Yan Nijeriya Shinkafa Da Sauran Kayan Da Ta Kwato

123
0

Don rage radadin yunwa da matsin tattalin arziki da rage tasirin tsadar kayan abinci a kasa, hukumar kwastam a Nijeriya, ta sanar da shirinta na raba kayan abincin da samu nasarar kwatowa.

Rahotanni sun rawaito cewa haramtattun kayayyakin abincin da jami’an hukumar suka kama sun hada da shinkafa da man gyada da taliyar yara da sauran kayayyaki da dama.

Hukumar, a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na kasa, Abdullahi Maiwada, ya rabawa manema labarai a ranar Talata, ta ce ta dauki matakin ne a don magance kalubalen da ake fuskanta a halin yanzu na tsadar kayan abinci a Nijeriya.

Ya ce, za a tabbatar da ingancin kayayyakin ga hukumomin da abin ya shafa za su iya amfani da su, sannan kuma za su isa ga ‘yan Nijeriya ta hanyar rarraba su a yankunan da hukumar kwastam ke gudanar da ayyuka a fadin Nijeriya.

Maiwada ya ce, za a bi hanyoyin da suka dace wajen raba kayan, za a tabbatar da gaskiya da adalci wajen rabon kayan ga jama’a.

Leave a Reply