Home Labaru Endsars: Lagos Ta Yi Karin Haske Kan Mutanen Da Za Ta Binne

Endsars: Lagos Ta Yi Karin Haske Kan Mutanen Da Za Ta Binne

78
0

Gwamnatin jihar Legas, ta yi karin haske a kan wasu labarai
da ta ce na bogi ne, cewa za ta birne mutane 103 da aka kashe
a Lekki Toll Gate lokacin zanga-zangar Endsars ta shekara ta
2020.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin ta musanta lamarin da cewa, mutane103 da aka rubuta a takardar an gano su ne a sassa daban-daban na jihar Legas.

Zanga-zangar Endsars dai ta girgiza Nijeriys, inda ta sa aka yi sauyi a aikin dan sanda, bayan masu fafutuka sun zargi jami’an tsaro da bude wuta a kan masu zanga-zanga a Lekki Toll Gate da ke Legas, inda ake zargin su da kashe mutane da dama.

A watan Disamba na shekara ta 2021, gwamnatin jihar Legas ta musanta cewa jami’an tsaro sun yi wa masu zanga-zanga kisan kiyashi, inda ta ce mutum daya ne kawai harbin bindiga ya samu lokacin zanga-zangar.

A sanarwar da gwamnatin jihar Legas ta fitar, ta ce wadanda za a birne ba a Lekki Toll Gate aka kashe su ba, gawarwaki ne da aka gano a sassa daban-daban na birnin sakamakon rikic.

Leave a Reply