Home Labaru El-Rufai Ya Ce Hare-Haren ‘Yan Bindiga Sun Fi Na Boko Haram Muni

El-Rufai Ya Ce Hare-Haren ‘Yan Bindiga Sun Fi Na Boko Haram Muni

152
0

Gwamnatin jihar Kaduna, ta ce an kashe mutane dubu 1 da 129 a fadin jihar Kaduna a shekarar da ta gabata, sannan an kiyasta cewa a kullum a kan sace mutane tara a fadin jihar.

Yayin da ya ke jawabi a wajen taron gabatar da rahoton tsaro na shekara ta 2021, gwamna Nasir Ahmed El-Rufa’i ya ce rahoton ya tabbatar da cewa akwai aiki a gaban mahukunta.

Ya ce ya kamata gwamnati ta dauki tsauraran matakan tsaro a kan hare-haren ‘yan-bindiga a yankin Arewa maso yammacin Nijeriya fiye da yadda ta yi a kan mayakan Boko Haram.

Rahoton tsaro na shekara ta 2021 da gwamnatin jihar Kaduna ta gabatar dai ya nuna cewa, kananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa da Igabi da Chukun da Zangon Kataf ne su ka fi adadin wadanda ‘yan-bindigar su ka hallaka a bara.

Leave a Reply