Majalisar Wakilai ta roƙi Gwamnatin Ingila ta sassauta hukuncin da aka yanke wa tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ike Ekweremadu, wanda aka kama da laifin yunƙurin yin dashen ƙoda ba bisa ƙa’ida ba.
Ɗan Majalisa Toby Okechukwu daga Jihar Enugu ne ya kawo hanzarin a cikin gaggawa kuma aka amince da hakan a zauren majalisar nan take.
Majalisar wakilai, ta roƙi Gwamnatin Ingila da kotun ƙasar ta tausaya wajen yanke wa Ekweremadu da matar shia da likitan su hukunci, sannan ta roƙi Gwamnatin Niajeriya ta sa baki wajen ganin ta damu da halin da Ekweremadu da iyalin sa ke ciki.
Idan dai ba a manta ba, a ranar 5 Ga watan Mayu na shekara ta 2022 ne aka kama Ike Ekweremadu a London, bisa zargin shi da yunƙurin cire ƙodar wani ƙaramin yaro domin a dasa wa wata ‘yar sa.














































