Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta mika wa Kotu bukatar kwace wasu kadarori 29 na kimanin naira biliyan daya mallakin Abdulrasheed Maina.
Idan dai za a iya tunawa, jami’an tsaro sun kama Abdulrasheed Maina ne a wani Otal da ke Abuja, yayin da ya shigo Nijeriya cikin sirri daga kasar Dubai.
Wasu kadarori a kasashen ketare da ake zargin na Maina an gano su ne a kasar Dubai.
Wata Majiya ta ce, daga cikin abubuwan da aka samu a hannun Maida da dan sa akwai layikan waya 31, da wayoyin tafi-da-gidan-ka guda 19.
Majiyar ta kara da cewa, akwai bayanan hannayen jari da kadarorin Maina na kasashen ketare, wadanda ke dauke da sunan dan sa maimakon na shi.
Rahotanni
sun ce, an gano kamfanin hayar motocin alfarma da masana’antar tsaftace
kayayyaki mallakin Maina da ke kasar Dubai, yayin da ake zargin kamfanin man
fetur da iskar gas na Ostrich mallakin shi ne.
You must log in to post a comment.