Home Labaru EFCC Ta Kammala Shirin Kama Wasu Gwamnonin Najeriya

EFCC Ta Kammala Shirin Kama Wasu Gwamnonin Najeriya

288
0

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta kaddamar da
gagarumin bincike a kan wasu gwamnoni da mataimakan su
da ke shirin mika mulki, sakamakon kawo karshen kariyar
tuhumar da su ke da ita kamar yadda doka ta tanada.

Wani bincike da Jaridar Premium Times ta gudanar, ya ce Hukumar EFCC ta baza komar ta domin kama wasu daga cikin gwamnonin da mataimakan su 28, wadanda ke shirin sallama da gidajen gwamnati a makon gobe.

Binciken ya ce, tuni hukumar EFCC ta bukaci takardun kadarorin da gwamnonin su ka cika kafin su fara aiki, wanda ya bayyana irin dukiyar da su ka mallaka a wancan lokaci, yayin da take dakon wadanda za su bada a yanzu domin yin nazari akan su.

Binciken Jaridar ya kara da cewa, hukumar EFCC ta kammala domin ganin gwamnoni ba su gudu sun bar Nijeriya ba bayan mika mulki ga wadanda za su gaje su a ranar litinin mai zuwa.

Leave a Reply