Home Labaru Bankwana: Buhari Ya Rantsar Da Sabbin Kwamishinoni 5

Bankwana: Buhari Ya Rantsar Da Sabbin Kwamishinoni 5

86
0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya rantsar da sabbin
kwamishinoni biyar a Hukumar Tsara Albashi ta Kasa
kwanaki biyar kafin ya sauka daga mulki.

Buhari ya ba su rantsuwar aikin ne gabanin fara taro Majalisar Zartarwa ta Kasa ta karshe a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Sabbin Kwamishinonin da aka rantsar sun hada da Hauwa Aliyu daga Jihar Jigawa, da Rakiya Haruna daga jihar Kebbi, da Isma’ila Agaka daga jihar Kwara, da Sanata Ayogu Eze daga jihar Enugu, da Peter Opara daga jihar Imo, da Kolawole Abimbola daga Jihar Oyo, da kuma Ayuba Ngako daga Yankin Birnin Tarayya Abuja.

A yayin zaman majalisar, Mataimakin Shugaban Kasa Yemi osinbajo ya mika rahoton kwamitin da ya jagoranta a kan inganta bangaren lafiya, domin samar da jadawali da nagartaccen tsarin kula da lafiya ga daukacin ‘yan Nijeriya cikin sauki.

Daga cikin shawarwarin kwamitin, akwai batun kara kudaden da ake ba bangaren daga kashi 10 cikin 100.

Leave a Reply