Home Labaru EFCC Ta Cafke ’Yan Yahoo 50 a Oyo Da Ondo

EFCC Ta Cafke ’Yan Yahoo 50 a Oyo Da Ondo

91
0

Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta sanar da
kama mutane 50 masu damfara ta yanar gizo da aka fi sani da
‘yan Yahoo a jihohin Ogun da Oyo.

A cikin wata Sanarwa da hukumar ta fitar, ta ambaci sunayen mutane 47 ciki har da wani ma’aikacin Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da aka kama a Abeokuta.

Sanarwar mai dauke da sa hannun Sakataren Yada Labarai na hukumar EFCC Wilson Uwujaren, ta ce a ranar Laraba, 14 ga watan Yuni ne aka yi nasarar kama mutane a maboyar su da ke Idi-Aba a birnin Abeokuta na Jihar Ogun.

Haka kuma, sanarwar ta ce an kama wasu mutane biyu a Unguwar Idi-Igba da ke birnin Ibadan a Jihar Oyo, sannan ‘yan sanda sun kama wani mutum daya a Ibadan aka mika shi ga hukumar EFCC.

Bayanai na cewa, daga cikin kayayyakin da aka samu a hannun wadanda ake zargin a Abeokuta har da kananan motoci 7 masu tsada, da wayoyin salula iri-iri masu yawa da na’urorin kwamfutar tafi-da-gidan-ka da agogunan hannu masu tarin yawa da tsada.

Haka kuma, daga cikin abubuwan da aka samu a hannun wadanda aka kama a Ibadan akwai kananan motoci biyu masu tsada, da wasu kayan da ba a fayyace yawan su ba.

Leave a Reply