Hukumar hana zambar kudi da karya tattalin arzikin kasa EFCC ta bayyana aniyar ta na gudanar da kwakkwaran bincike a kan zarge-zargen almundahana a bangaren wutar lantarkin Najeriya.
Shugaban Hukumar , Ola Olukoyede, ne ya bayyana haka yayin wata ganawa da ‘yan kwamitin majalisar wakilai kan yaki da cin hanci da rashawa a shelkwatar hukumar dake nan Abuja.
Ola Olukoyede ya nuna matukar damuwar sa kan kalubalen da ke ci gaba da addabar fannin tare da tabbatar wa kwamitin cewa hukumar EFCC ta dukufa wajen bankado duk wata badakala da ta shafi ƙudi.
Ya kuma bayyana cewa hukumar EFCC ta bankado wani al’amari mai cike da damuwa, inda a cikin shekara 20 da suka gabata.
babu wata ma’aikata ko hukumar gwamnati a Najeriya da ta aiwatar da kashi 20 cikin 100 na manyan ayyuka da aka zayyana a cikin kasafin kudin su.
Shugaban hukumar ta EFCC ya bayyana hakan a matsayin wani gagarumin cikas ga ci gaban Najeriya da samar da ababen more rayuwa ga ƴan ƙasa.














































