Home Labaru Dubu Ta Cika: An Kama Basarake Da Hannu A Garkuwa Da Mutane...

Dubu Ta Cika: An Kama Basarake Da Hannu A Garkuwa Da Mutane A Jihar Nasarawa

777
0

Jami’an rundunar ‘yan sanda ta jihar Nasarawa, sun kama dagacin kauyen Mangora Gina  da ke karamar hukumar Tunga a jihar Nasarawa.

Ana dai kama Dalhatu Abubakar ne bisa zargin sa da taimaka wa masu garkuwa da mutane, kamar yadda kwamishinan ‘yan sanda na jihar Bola Longe ya bayyana, yayin da ya ke gabatar da dagacin da wasu mutane 80 da ake zargi ga manema labarai.

Bola Longe, ya ce jami’an ‘yan sandan sun kama basaraken ne, bayan wasu bayanan sirri da su ka samu game da hannun sa a garkuwa da mutane da ake yi a yankin Loko na Nasarawa da Toto.

Ya ce kasurgumin dan ta’adda ne da aka dade ana labari kuma tuni ya kasance a jerin wadanda su ke nema ido rufe.

Kwamishinan ya cigaba da cewa, daga ranar 22 ga watan Oktoba zuwa watan Disamba na shekara ta 2019, hukumar ta kama mutane 46 da ta ke zargi da garkuwa da mutane, da kuma mutane 35 da ta ke zargi da zama ‘yan kungiyar asiri.

‘Yan sandan sun ce, sun samu bindigogi 9 da harsasai 34, da Keke NAPEP 3 da babura 2 da motoci uku daga wajen wadanda ake zargi.