Home Labaru Dokar Ta-Ɓaci Za Ta Kare Rikicin Kundin Tsarin Mulki – Lai Mohammed

Dokar Ta-Ɓaci Za Ta Kare Rikicin Kundin Tsarin Mulki – Lai Mohammed

15
0
Lai Muhammad

Gwamnatin tarayya ta sake jaddada matsayar ta, game da yunƙurin sa dokar ta-ɓaci a Jihar Anambra saboda tashe-tashen hankula.

A ranar Larabar da ta gabata ne, Ministan Shari’a Abubakar Malami ya za su iya sa dokar ta-ɓaci idan aka cigaba da kashe rayukan al’umma a jihar, jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa da Shugaba Buhari ya jagoranta a fadar sa da ke Abuja.

Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed, ya ce Malami ya bayyana hakan ne domin kauce wa rikicin kundin tsarin mulki.

Ya ce Ministan shari’a ya ce gwamnati za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen dawo da doka da oda a jihar Anambra da ma yankin kudu maso gabas baki daya, don ganin cewa ba a yi wasa da turakun dimokuraɗiyya ba.

Lai Mohammed, ya ce zaɓen gwamnan da za a yi ranar 6 ga watan Nuwamba ya na cikin turakun dimokuraɗiyya, ya na mai zargin ƙungiyar ‘yan tawaye ta IPOB da hana mutane zuwa makarantu da kasuwanni a jihar.