Home Labarai Diflomasiyya: Shugaba Tinubu Zai Halarci Bikin Rantsar Da Zaɓaɓɓen Shugaban Senegal

Diflomasiyya: Shugaba Tinubu Zai Halarci Bikin Rantsar Da Zaɓaɓɓen Shugaban Senegal

45
0

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyara ƙasar Senegal
don halartar bikin rantsar da zaɓaɓɓen shugaba Bassirou
Diomaye Faye.


Wata sanarwa daga fadar shugaban kasa, ta ce Tinubu zai koma gida ne a dai wannan rana da zarar an kammala bikin na birnin Dakar.


Shugaba Tinubu, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS), zai bi sahun shugabannin kasashen Afirka domin halartar bikin da za a yi a gobe Talata.\


Tinubu zai samu rakiyar ministan harkokin kasashen waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar da wasu manyan jami’an gwamnati.\


Sanarwar ta ce ana sa ran shugaba Tinubu zai dawo Najeriya da zarar an kammala rantsar da sabon shugaban na Senegal.

Leave a Reply