Home Labaru Diflomasiyya: Nijeriya Da Afrika Ta Kudu Sun Karfafa Alakar Da Ke Tsakanin...

Diflomasiyya: Nijeriya Da Afrika Ta Kudu Sun Karfafa Alakar Da Ke Tsakanin Su

166
0
Diflomasiyya: Nijeriya Da Afrika Ta Kudu Sun Karfafa Alakar Da Ke Tsakanin Su
Diflomasiyya: Nijeriya Da Afrika Ta Kudu Sun Karfafa Alakar Da Ke Tsakanin Su

Nijeriya da Afrika ta Kudu sun rattaba hannu a kan wata yarjejeniyar ba ‘yan kasuwa da malamai da dalibai da masu n balaguro tsakanin kasashen takardun Biza da za su shafe shekaru 10 suna aiki.

An cimma wannan yarjejeniyar ce a lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke karkare ziyarar da ya kai kasar Afrika ta Kudu.

Kasashen sun ce daukar mataki na karfafa alakar tattalin arziki da siyasa da kuma ala’adun da ke tsakanin su za su taimaka wajen yaukaka zamantakwar kasashen biyu.

Wasu karin batutuwan da shugabannin suka tattauna tare da cimma matsaya a kai, sun hada da musayar bayanan sirri da kuma kaddamar da wani shiri da zai rika ba su damar hango tashin hankali domin daukar matakin gaggawa.

Idan dai ba a manta ba, a cikin watan Satumba shugaban Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa ya aike da jakada na musamman zuwa kasashen Afrika da suka hada da Nijeriya da Nijar da Ghana da Senegal da Tanzania da Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo da kuma Zambia, domin kwantar musu da hankali kan hare-haren da ake kai wa baki yan kasashen da ke zaune a Afrika ta Kudu.