Home Labaru Difilomasiyya: Miji Ya Harbe Matar Sa ‘Yar Nijeriya A Italiya

Difilomasiyya: Miji Ya Harbe Matar Sa ‘Yar Nijeriya A Italiya

142
0

Gwamnatin tarayya, ta nemi a yi cikakken bincike a kan musabbabin kashe wata matar aure ‘yar Nijeriya mai suna Rita Amenze da mijin ta ya yi a kasar Italiya.


A cikin wata sanarwa da shugaban hukumar kula da ‘yan Nijeriya mazauna ketare Abike Dabiri-Erewa ya fitar a Abuja, ta bayyana kisan matar a matsayin lamari mara ɗaɗi.


Jakadan Nijeriya a Italiya Mfawa Omini Abam, da Dabiri-Erewa da ‘yan Nijeriya da ke zaune a kasar, sun bukaci hukumomin tsaron Italiya su binciki lamarin su kuma tabbatar an yi adalci.


Amenze dai ta shiga kasar Italiya ne a shekara ta 2017 ta hanyar Libya, kuma ana zargin mijin ta Pierangelo Pellizzar ne ya kashe ta bayan ta nemi kotu ta raba auren su.
Rahotanni sun nuna cewa, Pellizzar ya bindige ta ne a gaban abokan aikin ta.
Shugaban ƙungiyar ‘yan Nijeriya mazauna ƙasar Italiya Rowland Ndukuba ya yi Allah-Wadai da kisan, ya kuma gode wa ‘yan sanda da su ka kama wanda ya aikata kisan.

Leave a Reply