Majalisar dokoki ta jihar Nasarawa, ta dakatar da mataimakin shugaban marasa rinjaye Luka Zhekaba bisa zargin sa da hannu a ɗaukar malaman sakandare ba bisa ƙa’ida ba.
Kakakin majalisar Ibrahim Abdullahi ya sanar da haka, inda ya ce majalisar ta dakatar da Zhekaba ne bayan nazari a kan rahoton kwamitin ilimi dangane da ɗaukar malamai 366, da wasu 38 da aka gano cikin tsarin biyan albashi da aka ɗauka ba bisa ƙa’ida ba.
Kakakin majalisar, ya kafa kwamitin wucin gadi na mutane uku domin gudanar da bincike a kan wanda aka dakatar, tare da umurtar ya bada rahoto cikin makonni biyu.
Ibrahim Abdullahi, ya kuma bayyana Suleiman Yakubu Azara mai wakiltar mazabar Awa ta kudu a matsayin shugaban kwamitin.