Home Labaru Difilomasiyya: Dan Nijeriya Ya Ragargaza Motoci A Ofishin Jakadancin Nijeriya A London

Difilomasiyya: Dan Nijeriya Ya Ragargaza Motoci A Ofishin Jakadancin Nijeriya A London

371
0

Wani hasalallen dan Nijeriya ya afka wa ofishin jakadancin Nijeriya da ke birnin Landon a kasar Birtaniya, inda ya ragargaza motoci har guda bakwai.

Bisa ga bayanan da aka samu bayan aukuwar lamarin, an ce mutumin mai suna Jeffery Ewohime, ya garzaya ofishin jakadancin ne domin ya karbi Fasfon sa da ya mika domin a sabunta masa.

Rahotanni sun ce, a lokacin da ya isa ofishin da misalin karfe 2 na rana, sai ma’aikatan ofishin su ka ce ma shi lokacin karbar Fasfo ya wuce sai kuma gobe, amma Jeffery ya cije lallai sai an ba shi, inda daga nan aka nemi ya mika shaidar da aka ba shi lokacin da ya kai Fasfon na shi, amma ya ce ya ce ba ya dashi sannan ya fice a fusace.

Bayan dan wani lokaci sai ya koma ya rika farfasa gilasan motocin da ke ajiye a gaban ofishin jakadancin, ciki har da motar Jakadan Nijeriya a kasar Birtaniya da wasu motoci biyu a gefe, inda akalla ya barnata motoci bakwai, sannan tuni ‘yan sandan Birtaniya sun kama Jeffery Ewohime.