Majalisar wakilai ta soke dokar kayyadde shekarun neman aiki a ma’aikatun gwamnatin tarayya da sauran hukumomi, biyo bayan koke-koken da ‘yan Nijeriya ke yi a kan yadda wasu ma’aikatu ke sa dokar kayyade shekarun daukar ma’aikata.
‘Yan majalisar dai sun gabatar da dokar ne a karkashin jagorancin dan majalisa Sergius Ogun na jam’iyyar APC daga jihar Edo, da Babajimi Benson daga jihar Lagos.
Dokar, wadda aka karanta a zauren majalisar karo na biyu a shekara ta 2018, ta shiga babi na uku bayan karbuwar da ta samu daga ‘yan majalisa da kuma shugaban majalisar wakilai a lokuta da dama.
Majalisar ta ce ta gabatar da dokar ne, domin tabbatar da cewa ba a hana wa wani dan Nijeriya samun aiki saboda dalilai na shekaru.Daya daga cikin ‘yan majalisar da su ka amince da dokar, Timothy Ngolu Simon, ya ce dalilin da ya sa Majalisa ta ce a cire tsarin kayyade shekaru a mai’aikatun da ke son daukar ma’aikata shi ne, akwai alamun ana bin son zuciya kuma ana karya doka wajen kin daukar ‘ya’yan talakawa aiki.