Home Labaru Dattawa Sun Zargi Jonathan Da Cin Amanar PDP

Dattawa Sun Zargi Jonathan Da Cin Amanar PDP

205
0
Goodluck Jonathan, Tsohon Shugaban Kasa
Goodluck Jonathan, Tsohon Shugaban Kasa

Zauren dattawan jam’iyyar PDP, ya zargi tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da musayar nasarar jam’iyyar a zaben gwamnan jihar Bayelsa na ranar 16 ga watan Nuwamba.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, shugaban kungiyar Chief Benson Odoko ya zargi Jonathan da hada kai da shugabannin jam’iyyar APC a jihar Bayelsa.

Odoko ya yi ikirarin cewa, ko shakka babu Jonathan ya ci amanar jam’iyyar PDP, wadda ta kai shi matsayin mataimakin gwamna da gwamna da mataimakin shugaban kasa da kuma shugaban kasa baki daya.

Haka kuma, ya danganta ziyarar da Jonathan ya kai wa shugaba Buhari a fadar sa da ke Abuja, da cewa alama ce da ta nuna ya na yi wa APC aiki ne maimakon jam’iyyar sa.

Odoko, ya bukaci shugabancin jam’iyyar PDP su tanadi duk hukuncin da ya dace da Jonathan, musamman a kan yadda ya fito fili ya na murnar nasarar da abokan hamayya su ka yi a jihar Bayelsa.