Home Labaru Atiku Abubakar Ya Dawo Nijeriya Bayan Wasu Watanni A Kasar Waje

Atiku Abubakar Ya Dawo Nijeriya Bayan Wasu Watanni A Kasar Waje

373
0
Atiku Abubakar, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa
Atiku Abubakar, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya dawo Nijeriya bayan ya kwashe watanni a kasar waje, kamar yadda mai magana da yawun sa Paul Ibe ya bayyana wa manema labarai.

Paul Ibe, ya ce a ranar Talata, 26 ga watan Nuwamba Atiku zai isa jihar Adamawa, domin gaisuwar ta’aziyya ga iyalan wani hadimin sa da ya riga mu gidan gaskiya.

Bayan tafiyar sa zuwa kasar Dubai, shugaba Buhari ya samu nasara a kan Atiku da jam’iyyar PDP a kotun daukaka kara da kotun koli, inda ya ke kalubalantar nasarar Buhari a zaben shekara ta 2019.

Atiku da lauyoyin sa dai sun zargi Buhari da rashin kammala karatun sakandare, don haka su ke ganin bai cancanci ya tsaya takarar kujerar shugaban kasa ba.