Home Labarai Dan Takarar Nnpp Ya Nemi Kotu Ta Hana Inec Kammala Zaben Doguwa/Tudun...

Dan Takarar Nnpp Ya Nemi Kotu Ta Hana Inec Kammala Zaben Doguwa/Tudun Wada

114
0

Dan takarar kujerar majalisar wakilai na mazabar Doguwa da
Tudun Wada a karkashin Jam’iyyar NNPP Salisu Yusha’u, ya
bukaci kotu ta dakatar da Hukumar Zabe daga gudanar da
karashen zaben kamar yadda ta shirya.

Salisu Yusha’u, ya nemi kotu ta hana hukumar gudanar da karashen zaben ne kwanaki 10 kafin ranar 15 ga watan Afrilu kamar yadda hukumar ta tsara tare da sauran zabubbukan da ba su kammala ba.

A takardar karar da Salisu Yusha’u ya shigar ta hannun lauyan sa Adegboyega Awolomo, ya ce, hukumar zaben ba ta da ikon gudanar da karashen zaben alhalin ya shigar da karar kalubalantar sakamakon zaben a kotu.

Idan dai ba a manta ba, hukumar zabe ta ayyana zaben mazabar Doguwa da Tudun Wada da ke Jihar Kano a matsayin wanda bai kammala ba, saboda kuri’un da aka soke a zaben sun haura tazarar da ke tsakanin Salisu Yusha’u da Alhassan Ado Doguwa na jam’iyyar APC.

Leave a Reply