Home Labarai ‘Yan Binidga Sun Yi Garkuwa Da Basarake a Jihar Filato

‘Yan Binidga Sun Yi Garkuwa Da Basarake a Jihar Filato

72
0

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wani basarake mai daraja ta
ɗaya a jihar Filato.

Basaraken, wanda ‘yan bindigar su ka ɗauka a fadar sa mai suna Sunday Dajep, ya kasance hakimin al’ummar Mhiship da ke karamar hukumar Pankshin.

Wani ganau ya ce, ‘yan bindigar sun isa fadar sarkin ne da ke kusa da hanyar Mangu-Shendam da misalin karfe 11 na dare, inda su ka kutsa cikin fadar tare da yin awon gaba da shi.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Filato DSP Alfred Alabo ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce su na ci-gaba da bibiyar sawun ‘yan bindigar domin kama su da kuma kuɓutar da basaraken.

Leave a Reply