Home Labaru Damfara: ‘Yan Sanda Sun Kama Ma’Aikacin Banki A Jihar Oyo

Damfara: ‘Yan Sanda Sun Kama Ma’Aikacin Banki A Jihar Oyo

65
0
Police

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Oyo, ta kama wani ma’aikacin banki mai suna Adeyemi Tosin, bisa zargin kwasar naira miliyan 10 daga asusun wani abokin huldar bankin Oladele Adida Quadri.

Kakakin rundunar ‘yan sandan DSP Adewale Osifeso ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce Tosin ya saci kudin ne da sunan zai taimake shi a reshen bankin na Ibadan, sakamakon matsalar da ya samu wajen cire kudi.

Binciken ‘yan sandan bisa umarnin kwamishinar ‘yan sanda ta jihar Ngozi Onadeko, an gano yadda matsalar ta auku bayan Na’urar ATM ta hadiye katin Quadri a reshen su na Ibadan.

Quadri dai ya nemi taimakon ma’aikacin ne bayan ya shiga bankin ya kuma ba shi duk wasu bayanan sa, inda wanda ake zargin ya yi amfani da wannan damar ya bude sabon asusu, ya yi ta wawurar kudaden mutumin ya na zubawa a asusun sa.